in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zabe ta Rasha ta sanar da lashe zaben da shugaba Vładimir Putin ya yi
2018-03-24 12:55:04 cri
Shugabar hukumar zabe ta kwamitin tsakiyar kasar Rasha Ella Pamfilova, ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar a hukunce, inda shugaba mai ci Vładimir Putin ya lashe zaben, bisa samun kuri'un goyon baya na kashi 76.69%.

Daga bisani, Putin ya gabatar da jawabi ta bidiyo a yanar gizo daga fadar Kremlin, inda ya ce, za a mayar da bayanin gwamnati na shekara-shekara da aka gabatar a ranar 1 ga wata, a matsayin wani shirin ayyuka da za a aiwatar, wajen ci gaba da inganta yi wa tattalin arziki da al'ummar kasar kwaskwarima, ciki har da karfafa ingancin tattalin arziki ta hanyar kimiyya da fasaha, da kara kudin shiga na jama'ar kasar.

A ranar 18 ga wata ne kasar Rasha ta shirya zaben shugaban kasa karo na 7, inda 'yan takara 8 suka shiga. Bisa dokar zaben shugaban kasar, wanda ya samu kuri'un goyon baya da suka zarce kashi 50% shi ne ya yi nasara. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China