A yayin ganawar su, Li Keqiang ya nuna cewa, kasar Sin da kasashen Afirka, ciki har da Kamaru dukkansu kasashe ne masu tasowa, don haka suna da moriyar bai daya ta samun ci gabansu. Kana kasar Sin na samar da tallafi ga kasar Kamaru ne ba tare da sharudan siyasa ba.
Shi kuwa Li Zhanshu cewa ya yi, sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar na fatan karfafa cudanya ta sada zumunta tare da majalisar dokokin Kamaru. Kuma a cewar sa kamata ya yi, hukumomin dokokin kasashen biyu, su kara nuna goyon baya ga juna a fannin siyasa, da kyautata muhallin hadin kai, da dai sauransu.
A nasa bangaren, Paul Biya ya ce, kasarsa na matukar yabawa manufar kasar Sin kan kasashen Afirka. Za kuma ta ci gaba da kokarin zurfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu, don ciyar da dangantakarsu gaba. (Bilkisu)