in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwa game da halin da ake ciki a DRC
2018-03-23 12:32:53 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayyana matukar damuwa sakamakon mummunan tabarbarewar yanayin da ake fama da shi a Jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), inda ya ce, halin da ake ciki ya yi matukar tsananta musamman a wasu sassan kasar.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kwamitin sulhun MDDr ya kuma bayyana damuwa game da karuwar mutanen da rikicin ya tilasawa zama a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar, wanda ya ninka har sau biyu idan aka kwatanta da shekarar bara wato ya zarta mutane miliyan 4.49.

Game da wannan batu, kwamitin sulhun MDD ya jaddada bukatar shawo kan matsalar kungiyoyin masu dauke da makamai dake cigaba da haifar da barazana ga zaman lafiyar kasar, don haka kwamitin yake bukatar a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe wanda zai kushi dukkan bangarorin kasar, wanda ake ganin zai iya kasancewa a matsayin wani muhimmin matakin da zai kawo dauwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a DRC.

Kwamitin ya bayyana damuwa sakamakon karuwar tabarbarewar yanayin samun damar shigar da kayan tallafi a yankin gabashin DRC, sakamakon rashin tsaro da tashe-tashen hankula a yankin, da kuma cigaba da kaddamar da hare hare da ake yi kan kayan tallafin da kuma jami'an bada agajin a yankin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China