in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
May, Merkel da Macron sun kalubalanci Rasha game da batun mutuwar jami'in leken asiri
2018-03-23 12:23:10 cri

Shugabannin kasashen Birtaniya, Jamus da Faransa suna cigaba da nunawa Rasha yatsa game da zargin da ake mata kan mutuwar jami'in leken asirin Birtaniya wanda ake zargin ya mutu ne ta hanyar guba, sai dai Moscow ta sha musanta cewa ba ta da hannu a zargin da ake mata.

Bayan da firaministar Birtaniya Theresa May ta gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a lokacin taron kolin shugabannin tarayyar Turai a Brussels, mai magana da yawun fadar mulkin Birtaniya ya bayyana cewa, May ta yiwa takwarorinta cikakken bayani game da binciken da aka gudanar kan wannan batu.

A lokacin ganawar tasu, May ta bayyana cewa, akwai kanshin gaskiya game da sakamakon da aka samu wanda ya nuna cewa, an yi amfani da sinadarai masu guba samfurin Novichok wanda Rashar ta kera, bayan da wasu tawagar masana kimiyya na duniya suka gudanar da bincike kan lamarin, in ji kakakin fadar mulkin Birtaniya.

Jami'in ya ce, Birtaniya da Jamus da Faransa sun nanata cewa, babu wani sauran bayani da ake bukata don tabbatar da cewa, Rasha na da hannu wajen aikata laifin.

Shugabannin uku sun kuma amince zasu cigaba da zama kan matsayinsu game da Rasha kan wannan batu kuma za su cigaba da tuntubar juna a wasu kwanaki masu zuwa a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China