in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijerita ta ba da tabbatacin har yanzu kungiyar Boko Haram na rike da daya daga cikin 'yan matan Dapchi
2018-03-23 10:44:23 cri

Gwamnatin kasar Nijeriya ta tabbatar da cewa, akwai yarinya guda cikin 'yan matan sakandaren Dapchi da har yanzu ke hannun kungiyar Boko Haram.

Gwmanatin ta bayyana sunanan yarinyar a matsayin Leah Sharibu, inda yanzu haka ana kokarin ganin an mai da ita ga iyayenta lami lafiya.

Kungiyar Boko Haram ce ta sace Leah Sharibu tare da wasu 'yan mata 109 daga kwalejin 'yan mata na Dapchi dake yankin arewa maso gabashin kasar a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Jimilar 'yan mata 104 ne kungiyar ta mayar garin Dapchi a ranar Laraba da ta gabata biyo bayan yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, 'yan ta'addan sun rike da yarinyar guda ne saboda ta ki musulunta.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar na cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari na sane da hakkin da aka rataya a wuyansa karkashin kundin tsarin mulki, na kare dukkan 'yan Nijeriya, ba tare da la'akari da addini ko kabila ko yanki ba, kuma ba zai yi watsi da wannan nauyi ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China