in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afrika na da muhimmanci ga muradun ci gaba masu dorewa
2018-03-23 09:44:32 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya ce, rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afrika, mataki ne mai muhimmanci da zai kai ga cimma muradun ci gaba masu dorewa wato SDGs tare da ajandar nahiyar ta tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

A jawabinsa na taya murna, Antonio Guterres ya jadadda cewa, a shirye baki daya tsarukan majalisar suke su mara baya ga nahiyar a kokarinta na fara amfani da yankin ciniki mara shinge a cikin watanni masu zuwa.

Shugabannin kasashen Afrika 44 ne suka rattaba hannu a ranar Laraba da ta gabata a birnin Kigalin Rwanda, kan yarjejeniyar kafa yankin ciniki mara shinge mafi girma a duniya.

A cewar hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta MDD, yarjejeniyar na da damar bunkasa cinikayya a cikin nahiyar da kashi 52.3 ta hanyar kawar da harajin shigar da kayayyaki kasashe, inda zai kuma rubanya cinikayyar idan aka rage matakan cinikayya masu tsauri.

Ana sa ran sana'o'i kanana da matsakaita ne za su fi amfana daga yankin, wandada su ne suka mamaye kaso 80 na kasuwanci a nahiyar.

A cewar Guterres, ci gaban harkokin masana'antu da ciniki cikin yanci da nahiyar ta gabatar, abubuwa ne da za su inganta ayyukan juna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China