Cikin wata sanarwa da ofishin WHO ya fitar, an bayyana cewa ma'aikatar lafiya, da gwamnatocin gundumomin kasar ta Uganda, na aiki tare da hukuma mai lura da 'yan gudun hijira ta MDD, da kuma asusun gaggawa na tallafawa kananan yara na MDD, da hukumar WHO, da kungiyar ba da agajin jin kai ta Red Cross mai aiki a Uganda, da sauran abokan hulda, domin tallafawa 'yan gudun hijirar.
A kalla 'yan gudun hira 50,000 ne daga lardin Ituri na jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, ke neman mafaka a kasar Uganda a wannan shekarar kadai, tun bayan barkewar tashin hankali a ranar 17 ga watan Disambar bara.