in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kamaru sun amince da fadada alakar dake tsakanin su
2018-03-22 20:52:57 cri

Kasashen Sin da Kamaru sun bayyana aniyar fadada kawance da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, a kokarin kara inganta huldar da ke kasashen biyu.

An fadi hakan ne yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Kamaru Paul Biya, a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, shugaba Biya shi ne shugaba na farko daga kasashen Afirka da ya kawo ziyara a nan kasar Sin a bana, shi ne kuma shugaba na farko na ketare da ya kawo ziyara Sin, bayan kammalar taruka biyu na Sin wato taron NPC da na CPPCC. A cewarsa, kasar Kamaru kawar kasar Sin ce a nahiyar Afirka, kuma Sin na fatan zurfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu, tare kuma da ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba. Baya ga haka, Xi Jinping ya nuna cewa, duk da yake ana samun sauye-sauye a duniya, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka.

A nasa bangaren, Biya ya bayyana cewa, kasar sa ta yaba wa shawarar 'Ziri daya da hanya daya" wadda Sin ta gabatar, tana kuma goyon bayan hadin kan kasashen Sin da Afirka bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya kara da cewa, kasashen Kamaru da Sin na da moriya da matsayi ta bai daya kan harkokin duniya. Kaza lika kasarsa na fatan karfafa cudanya da hadin kai da Sin bisa tsarin bangarori da dama, ciki har da MDD. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China