in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara kudin ruwan ajiya a Amurka
2018-03-22 11:20:29 cri
Asusun tarayyar kasar Amurka AFRC ya sanar a jiya Laraba da cewa, za a kara adadin kudin ruwan ajiya a bankunan kasar zuwa tsakanin kashi 1.5% da kashi 1.75%. Hakan ya kasance karon farko a bana, da asusun ya daga matsayin kudin ruwan ajiyar a bankunan kasar. Matakin da aka ce zai biya bukatun kasuwanni.

Asusun tarayyar kasar Amurka ya sanar da lamarin ne a wajen wani taron nuna manufofin harkar kudi. A cewar asusun, tattalin arzikin kasar Amurka ya samu ingantuwa a watannin baya. Kana matakin da aka dauka a wannan karo zai taimakawa karuwar tattalin arziki da samar da guraben aikin yi.

An kara da cewa, cikin watanni masu zuwa, za a kara samun hauhawar farashin kayayyaki a kasar Amurka, don haka asusun zai mai da cikakken hankali kan batun.

Haka kuma, asusun tarayyar kasar Amurkar na sa ran ganin karin ci gaban tattalin arzikin kasar Amukra a shekarun bana da badi, da karuwar guraben ayyukan yi a kasuwannin kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China