A jiya Laraba, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta kira wani taro na musamman domin bayyana yanayin da ake ciki wajen bin bahasin batun, inda ta gayyaci wasu jami'an diplomasiyya na kasashen waje dake kasar Rasha. Bangaren Rasha ya ce, sai an ba shi damar gudanar da bincike kan lamarin, kafin ya iya samun damar gabatar da wani sakamako. Haka kuma, ya nanata cewa, ba shi da hannu a cikin batun, tun da lamarin ba zai taimaka wajen karfafa tsaron kasar Rasha ba.
Kafin haka, fadar shugabancin kasar Amurka ta "White House" ta gabatar da wani bayani a jiya Laraba cewa, shugaban kasar Donald Trump ya riga ya buga waya ga takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron, inda suka tattauna wajibcin tilastawa kasar Rasha daukar nauyin wannan batu, kuma sun nuna niyyar rufa wa kasar Birtaniya baya.(Bello Wang)