in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sansanin sojan kasar Jamus a Nijar sansani ne na tsayawa domin jigila ta sararin sama
2018-03-22 09:56:44 cri
Jakadan kasar Jamus dake Nijar Dokta Bern Von Munchow-Pohl ya kira wani taron manema labarai a ranar Laraba da yamma, taron da ya maida hankali kan labaran da wasu kafofin yada labarai suke watsawa game da kasancewar sojojin kasar Jamus a Nijar.

Jami'in diflomasiyyar kasar Jamus ya yi amfani da wannan dama domin kawo karin haske da zummar bada cikakken bayani ga al'ummar kasar Nijar da kuma duniya. Ba tare da wani luge luge ba, jakadan Jamus ya jaddada cewa, sansanin sojan da kasarsa take da shi a Nijar, sansani ne kawai na tsayawa domin tafiyar da jigila ta sararin sama dake kunshe da sojoji 50, dukkansu kuma kwararru.

Haka kuma ya kara tabbatar da cewa, wannan sansanin soja an kafa shi ne bisa tsarin ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali domin tabbatar da hidimar kai kayayyaki, kwashe sojojin Jamus da suka ji rauni dake birnin Gao na kasar Mali.

Haka zalika kafa sansanin tsayawa na cikin tsarin yarjejeniyar jibge sojoji na wucin gadi da aka sanya wa hannu tsakanin gwamnatin Nijar da gwamnatin Jamus, in ji mista Bern Von Munchow-Pohl. (Mamane Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China