An ce, jami'ar Nairobi ta kasar Kenya, da majalissar cudanyar al'adu tsakanin Sin da Afirka ta Kenya ne suka gudanar da aikin tare, kuma mahalarta aikin daga bangaren Sin sun hada da masu aikin fasaha a fannonin zane-zane, da sassaka, da kuma tsare-tsare da dai sauransu, wadanda suka zo daga jami'ar Tsinghua da ma sauran wasu jami'o'i da kwalejojin kasar Sin.
Shugaban tawagar wakilan masu ayyukan fasaha ta kasar Sin Zhu Guizhou ya ce, an gudanar da aikin ne da nufin yada ra'ayin hadin kai da zumunci tsakanin bangarorin dake kan hanyar siliki, kana da yin cudanyar al'adu a tsakanin Sin da Kenya, matakin da zai aza harsashi mai kyau na samar da goyon bayan jama'a a fannin zurfafa hadin kai. (Bilkisu)