in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ai a Afrika sun lashi takobin shigar da 'yan gudun hijra cikin tsarin ilimi
2018-03-21 10:08:19 cri
Manyan jami'an gwamnati da masana a Afrika, sun sabunta kudurinsu na sanya wasu manufofi a bangaren ilimi, wadanda za su cimma bukatun matasa 'yan gudu hijra.

Jami'an da suka bayyana haka yayin wani taron yanki a Nairobin Kenya, sun bayyana cewa, daukar matakan suka dace da wadanda aka bari a baya ta fuskar ilimi, shi ne tubalin tabbatar da wadanda rikici ko annoba ya aukuwa sun samu damar samun ingantaccen ilimi domin farfado da rayuwarsu.

Da take gabatar da jawabin bude taron, Sakatariyar gwamnatin Kenya mai kula da harkokin ilimi Amina Mohammed, ta ce samun ilimi ga matasa 'yan gudun hijira muhimmin abu ne da zai inganta gudummawarsu wajen sake gina kasashensu da rikici ya dai-daita.

Ta ce akwai bukatar daukar managartan matakan kariya da magance tasirin rikice-rikice a kan ilimin matasa, tana mai cewa gudummawarsu wajen sake gina kasashensu da rikici ya lalata abu ne da ba zai misaltu ba.

Sakatariyar ta ce matasa 'yan gudun hijira da suka yi karatu, sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a kasashen da suka fuskanci tashin hankali a yankin kahon Afrika.

Ma'aikatar ilimi da hukumomin MDD masu kula da ilimi da yara da harkokin 'yan gudun hijira ne suka shirya taron na yini 4 ga yankin kahon Afrika, kan tsarin ilimi yayin shiryawa tunkarar rikici ko annoba da kuma shigar da 'yan gudun hijira cikin tsare-tsaren ilimi.

Mahalarta taron sun amince cewa akwai bukatar sake nazarin dabarun bunkasa ilimin matasa 'yan gudun hijira tare da kara gudummawarsu ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasashensu da ma kasashen dake ba su mafaka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China