in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya bukaci gwamnatocin Afrika su bada fifiko ga bangaren sufurin jiragen sama
2018-03-21 09:44:17 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bukaci gwamnatocin Afrika da su sanya fannin sufurin jiragen sama cikin bangarorin da suke baiwa fifiko a tsarin ajandojinsu na ci gaban kasa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a babban taron shekara-shekara na kungiyar masu kula da harkokin sufurin jiragen sama ta kasa da kasa wato (IFATCA), karo na 57.

Taron na kwanaki biyar, wanda ke gudanar tsakanin ranakun 19 zuwa 23 ga watan nan na Maris a Accra, babban birnin kasar Ghana, ya samar da wani dandali na musayar ilmi game da halin da ake ciki a yanzu a fannin sufurin jiragen saman.

Akufo-Addo ya ce, fannin sufurin jiragen sama wani muhimmin ginshiki ne wajen cimma nasarar ajandar AU na samar da dawwamammen ci gaban nahiyar Afrika nan da shekarar 2063, wanda aka tabo batunsa a taron kolin na kungiyar AU da ya gabata a Habasha, kungiyar ta sha alwashin kafa tsarin kasuwancin bai daya a harkokin sufurin jiragen sama a Afrika wato (SAATM), wanda ake da burin zai taimaka wajen inganta tsarin sufurin jiragen sama a tsakanin kasashen na Afrika, kuma zai daga martabar shiyyar.

A cewarsa, samar da ingantaccen tsarin kwarewa wanda kuma ya dace da matsayi irin na kasa da kasa muhimmin abu ne wajen cimma nasarar shirin na SAATM, ya kara da cewa hukumar kula da sufurin jiragen saman Afrika tana yin aiki tare da takwarorinta na duniya wajen kyautata inganci da tsaron fannin sufurin jiragen saman na Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China