in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya lashe babban zaben kasar Rasha
2018-03-19 13:38:08 cri

Da safiyar yau Litinin ne babban kwamiti mai kula da harkokin zabe na kasar Rasha, ya sanar da sakamakon kidayar kuri'un da yawansu ya kai kashi 95 cikin dari, bisa jimillar kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar, inda aka bayyana cewa, shugaba mai ci Vladimir Putin, yana kan gaba a zaben da kuri'un da ya samu suka kai kashi 76.56 cikin dari. Lamarin da ya shaida cewa, Putin ya riga ya lashe babban zaben kasar.

Shugaba Putin ya nuna godiya ga jama'arsa da suka taru a filin Red Square da ke birnin Moscow fadar mulkin kasar don taya shi murna, inda ya furta cewa, a yau dukkan masu zabe na kasar Rasha sun zamo tsinstiya madaurinki daya. Ya ce abu mafi muhimmanci shi ne burin da ake da shi na kara hadin kan 'yan kasa don samun ci gaba tare.

Shugaban ya kara da cewa, Rasha za ta kara azama wajen tinkarar dukkan kalubalolin da ke gabanta, da ma warware matsaloli iri daban daban da ke addabarta.

A wani ci gaban kuma, yayin da yake amsa tambayar da wakilin kamfanin dillancin labaru na kasar Sin na Xinhua ya yi masa a gun taron manema labarai, Shugaba Putin ya sake taya wa Shugaba Xi Jinping murnar zama shugaban kasar Sin. Ya kuma kara da cewa, kasar Rasha za ta habaka hadin gwiwa tare da kasar Sin bisa iyakacin kokarinta, ciki har da hadin gwiwarsu a fannonin zirin tattalin arziki na hanyar siliki, da kawancen kasashen Turai da Asiya ta fuskar tattalin arziki, ganin yadda bangarorin biyu ke da mudaru na bai daya a wannan fanni. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China