Jaridar ta ruwaito a jiya cewa, kokarin da kasar Sin ta yi, ya yi kyakkyawan tasiri kan samar da sauyi a zirin Korea.
Har ila yau, ta ce duniya baki daya, musammam nahiyar Afrika, na amfana sosai daga hadin gwiwa da kasar Sin dake kasancewa bisa gaskiya da adalci da daidaito da moriyar juna da aminci da kawance da kuma mara baya ga juna.
Jaridar ta kara da bayyana hadin gwiwa da kasar Sin a matsayin muhimmiya, wadda ke kara fahimtar juna da bada damar cimma matsaya guda da kuma kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gida. (Fa'iza Mustapha)