in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun bukaci Nijeriya ta yi amfani da damarmakin shirin "Ziri daya da hanya daya"
2018-03-17 10:25:59 cri
Wasu ayarin kwararru sun bayyana cewa, Nijeriya na da dimbin damarmaki da za ta amfana da su daga shirin "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar.

Yayin wata tattaunawa da ta gudana jiya a Abuja babban birnin kasar, kwararrun sun bukaci gwamnatin kasar ta kafa wata hukuma da ta kunshi dukkan ma'aikatun gwamnati, domin samar da dabarun da kasar za ta yi amfani da su wajen cin dimbin gajiyar dake tattare da shirin.

Shirin da ya kunshi hanyar siliki ta kan tudu da hanyar siliki ta cikin ruwa ta karni na 21, na da nufin hada nahiyar Asia da Turai da kuma kasashen Afrika ta yadda za a cimma moriya tare.

Kwararrun da suka hada da malamai da 'yan jarida da 'yan siyasa da masana tattalin arziki, sun ce lokaci ya yi da Nijeriya za ta yi kyakkyawan amfani da damarmakin da kasar Sin ke samarwa domin ta inganta tattalin arzikinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China