Shugaban kwamitin majalisar mai bada shawara kan ci gaban kasashe Jose Antonio Ocampo, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin gagarumi da zai shiga tarihi.
Ya shaidawa manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, kasashe 5 ne kadai aka yaye daga jerin, tun bayan bullo da rukunin kasashen da suka fi kowanne koma baya ta fannin ci gaba cikin shekaru 47 da suka gabata, inda ya ce a yanzu ma akwai kasashe 2 da suka hada da Angola da Vanuatu dake kan hanyar fita daga jerin.
Sai hukumar kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewa ta MDD da ma daukacin zauren majalisar sun amince, kafin a yaye kasashen 4. Kana Sai an ba kasa wa'adin shekaru 3 kafin a cireta daga jerin a hukumance.
A cewar Jose Ocampo, shawarar kwamitin ta biyo bayan karuwar kudaden shiga a dukkan kasashen tare da ingantuwar harkokin ilimi da na kiwon lafiya.
A kan tantance jerin kasashe mafi koma baya ta fuskar ci gaba ne bisa sharuda 3 da suka hada da harkokin ilimi da kiwon lafiyar al'umma da karfin tunkarar barazanar tattalin arziki da kuma kudin shiga na kowanne dan kasar. kuma sai kasa ta cika 2 cikin sharudan 3, har sau 2 a jere yayin nazarin kasashen da ake yi bayan shekaru 3-3, kafin a duba yiwuwar yayeta.
Yanzu haka dai, kasashe 47 ne mafi koma baya a duniya, inda suke wakiltar mutane biliyan 1. Kasashe 33 daga jerin sun kasance a nahiyar Afrika, inda Asiya ke bi mata da kasashe 9 yayin da Oceania ke da 4. (Fa'iza Mustapha)