in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'i: Madatsar ruwa da kasar Sin ta gina a Rwanda zai taimakawa bangaren noman kasar
2018-03-16 09:51:36 cri
Jami'in dake kula da aikin gina madatsar ruwan Muyanza da kamfanin kasar Sin na CGC ya gina a Rwanda Esdras Byringiro ya ce, madatsar ruwan da aka kammala ba da dadewa ba za ta taimakawa manoma wajen noma amfanin gonan da za su fitar zuwa kasashen waje.

Ita dai madatsar ruwan da tsayinta ya kai mita 26 tana gundumar Rulindo ne dake lardin arewacin kasar. Kuma kamfanin kasar Sin na CGC ya yi aikin gina ta,yayin da bankin duniya kuma ya ba da kudin aikin.

Jami'in wanda ya bayyana hakan jiya Alhamis yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce madatsar ruwan dai ita ce ta biyu mafi tsayi a Rwanda, kana madatsar ruwa mafi girma a fannin aikin gona.

Ana sa ran madatsar ruwan ta adana ruwan da zai wadatar da eka 1,100 a duk tsawon shekara, ta yadda zai amfani dukkan rukunonin manoma, ciki har da kanana da matsakaitan manoma da ma masu noma na kasuwanci. Ana ganin filayen dake tsaunuka da madatsar ruwan za ta samarwa ruwa shi ne mafi girma a kasar ta Rwanda.

Aikin gina madatsar ruwa, da shiriye-shiryen noman rani da farfado da filaye masu dausayi da suka bushe da kamfanonin kasar Sin suka gudanar a kasar, sun taimakawa gwamnatin Rwandar wajen bullo da ayyukan noman rani a sassa daban-daban na kasar, matakin da ya kara samar da amfanin gona, da karin kudin shiga ga manoma baya ga yadda rayuwar manoma a kasar ta inganta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China