Shugaban hukumar raya al'adu ta kasar Olusegun Runsewa ne ya bayyana haka a jiya, inda ya ce dukkan magoya bayan kungiyar za su sanya tufafi daban-daban na gargajiya tare da daga tutar kasar a ranekun da Super Eagles din za su buga wasa.
Ya ce nan bada dadewa ba za bude shafin website ta yadda magoya bayan za su shiga.
Ya kara da cewa wannan al'ada ce da aka saba yi a sauran kasashen duniya, inda ya ce ba za a bar Nijeriya a baya ba.
Kasar Rasha ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA ta bana da za a yi tsakanin ranekun 14 ga watan Yuni da 15 ga watan Yuli, inda Nijeriya ta fada rukuni na D tare da kasashen Argentina da Crotia da Iceland. (Fa'iza Mustapha)