in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP ya yabawa gudummawar kasar Sin ga 'yan gudun hijirar Jordan
2018-03-15 10:53:34 cri
Daraktan shirin samar da abinci na MDD a Jordan Mageed Yahia, ya jinjinawa tallafin da kasar Sin ke baiwa 'yan gudun hijirar kasar Syria masu samun mafaka a Jordan.

Mr. Yahia ya bayyana hakan ne, yayin bikin kammala shirin Sin na bada tallafi ga 'yan gudun hijirar. Jami'in ya ce tallafin na Sin ya saukaka ayyukan WFP a yankin baki daya.

A nasa tsokaci, jakadan Sin a kasar ta Jordan Pan Weifang, ya ce kasar sa ta ba da taimako a sassa da dama, wadanda suka hada da samar da tsaftacaccen ruwan sha, da muhalli da gina tituna da dai sauran su.

Daga nan sai ya alkawarta karin tallafin kasar Sin ga kasar Jordan, a fannin bunkasa tattalin arziki, da kuma dabarun warware matsalolin 'yan gudun hijirar Syria dake fakewa a kasar.

A watan Satumbar shekarar 2016 ne dai kasar Sin da WFP, suka sanya hannu kan yarjejeniyar tallafi ta dalar Amurka miliyan 2, wadda ta kunshi samar da sinadaran abinci masu gina jiki, ga 'yan gudun hijirar Syria dake zaune a kasashen Lebanon da Jordan, inda Jordan ta samu dala miliyan daya da rabi, cikin jimillar kudaden da aka ware domin aikin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China