in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya: Yawan masu gudun hijira daga Habasha ya haura mutum 8,500
2018-03-15 10:47:16 cri
Sama da mutane 8,500 ne suka tsallaka iyakar kasar Habasha don samun mafaka a kasar Kenya, sakamakon halin kuncin rayuwa da ke raba dubban jama'a da muhallan su.

Kungiyar agaji ta Red Cross dake aiki a Kenya ce tabbatar da hakan, tana mai nuna damuwa game da karuwar mutane dake cikin matsananciyar bukatar taimako, a daidai gabar da karin iyalai ke ketara garin Moyale dake kan iyakar Habasha zuwa arewacin kasar Kenya.

Da yake karin haske game da halin da ake ciki, babban sakataren kungiyar ta Red Cross a Kenya Abbas Gullet, ya ce kungiyar na matsa kaimi wajen tallafawa 'yan gudun hijirar dake tsallakawa zuwa Kenya. Cikin wata sanarwa, Mr. Gullet ya ce ana gudanar da wannan aiki ne ta hanyoyi da dama wadanda za su amfani 'yan gudun hijirar.

A wani batu mai nasaba da hakan kuma, wasu 'yan gudun hijirar kasar ta Habasha sun gamu da ajalin su, bayan da dakarun gwamnatin kasar Habashan suka bude musu wuta a ranar Asabar, bisa zaton cewa mambobi ne na haramtacciyar kungiyar 'yan tawayen Oromo Liberation Front ko (OLF) a takaice. 'Yan gudun hijirar sun gamu da ajalin su ne a kusa da garin Moyale dake kan iyakar kasar da Kenya.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sojoji sun yiwa yankin Moyale dirar mikiya, a wani mataki na dakile yiwuwar kwararar mambobin haramtacciyar kungiyar ta OLF cikin kasar ta Habasha. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China