'Yayansa sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa, mahaifinsu ya rasu a wannan rana. Sanarwar ta kara da cewa, Hawking mashahurin masani ne, kuma aikinsa da nasarorinsa za su kawo babban tasiri ga duniya a shekaru da dama masu zuwa.
An haifi Hawking a ranar 8 ga watan Janairu na shekarar 1942 a birnin Oxford dake kasar Birtaniya, kuma masani ne kan ilmin sararin samaniya da aikin kira, yana kuma nazari kan ra'ayin sararin samaniya da Black Hole. Ana daukar sa a matsayin masani kan ilmin aikin kira ko kimiyya mafi kwarewa tun bayan Albert Einstein. (Zainab)