in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya kori jami'in shirin afuwa na yankin Niger Delta
2018-03-14 09:58:16 cri
A jiya Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori Paul Boroh a matsayin jami'in shirin Amnesty na yin afuwa ga tsoffin mayakan tsagerun yankin Niger Delta na ofishin shugaban kasa.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, shugaba Buhari, ya amince da nada Charles Dokubo don maye gurbin tsohon jami'in.

Shugaban Najeriyar ya umarci babban mai bashi shawara kan harkokin tsaro (NSA) da ya gudanar da cikakken binciken game da shirin na Amnesty tun daga shekarar 2015 zuwa yau.

Fadar shugaban kasar ta kara da cewa, za'a gudanar da wannan binciken ne musamman game da zarge-zargen almundahanar kudade da ake zargin an tafka, wanda shine ke kawo nakasu ga shirin yin afuwa ga tsagerun yankin, wanda ofishin shugaban kasa ya bullo dashi.

A watan Yunin shekarar 2009 ne, gwamnatin Najeriyar ta yi tayin afuwa ga tsagerun yankin na Niger Delta mai arzikin mai, inda ta bukace su dasu aje makamansu zuwa ranar 4 ga watan Oktoba a matsayin wani mataki da zai kawo karshen zaman tankiya a yankin, wanda yake haifarwa kasar tafka mummunar hasara na biliyoyin daloli na kudaden shigarta wanda take samu daga danyen man da take fitarwa kasashe ketare.

Daruruwan matasan tsagerun yankin sun aminci da tayin da gwamnatin Najeriyar tayi musu, kuma sun rungumi shirin domin kawo karshen fada a yankin mai arzikin mai da ya jima yana fuskanta tashin hankali.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China