Yau Talata ne Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yi bakin ciki sosai da samun labarin rasuwa da jikkatar wasu mutane sanadiyar hadarin jirgin sama a kasar Nepal, tare da mika ta'aziyya dangane da wadanda suka rasa rayukansu a hadarin.
A jiya ne, wani jirgin saman fasinja dauke da mutane 71 da ya tashi daga birnin Dhaka na kasar Bangladesh zuwa kasar Nepal ya wuce titin saukarsa inda ya fadi ya kuma kama da wuta, inda mutane 49 suka mutu, kana an kai mutane 22 da suka ji rauni zuwa asibiti. (Tasallah Yuan)