Rahotanni da kafofin watsa labaru na kasar Nepal suka bayar, na cewa mutane 49 ne suka mutu,kana an kai mutane 22 da suka ji rauni zuwa asibiti, wasu daga cikinsu sun ji munanan raunuka
Jirgin saman da ya fadi samfurin BS-211 mai daukar mutane 78 mallakin kamfanin US-Bangla Airline ne. Jirgin dai yana dauke da fasinjoji 67 da kuma ma'aikata 4, ciki har da mata 28 da yara 2 'yan kasar Bangladesh. (Zainab)