in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin wajen Amurka ya kammala ziyarar da ya kai Afrika
2018-03-13 09:54:07 cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya kammala ziyarar aiki ta farko da ya kai kasashen Afrika 5 a jiya Litinin, bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari.

Yayin ganawar, shugaba Buhari da Rex Tillerson sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki da harkokin zuba jari da kuma babban zaben kasar na shekarar 2019.

Wata sanarwa da gwamnatin Nijeriya ta fitar ta ruwaito cewa, wani muhimmin batu da tattaunawar tasu ta tabo shi ne, na sace 'yan matan sakandare 110 da aka yi a garin Dapchi dake arewa maso gabashin kasar.

Tillerson ya ce, Amurka za ta taimaka wa Nijeriya da kayayyakin kiyaye tsaro na zamani da musayar bayanan sirri a kokarinta na ganin an dawo da 'yan matan.

Yayin taron manema labaran da aka yi a Abuja, babban birnin kasar, sakataren harkokin wajen Amurkan ya bayyana Nijeriya a matsayin kasa mai muhimmanci ga Amurka, yana mai cewa, Amurkar za ta mara baya ga damarmakin fadada tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce, akwai bukatar kara yawan cinikayyar dake tsakanin kasashensu biyu, inda ya ce, darajar cinikayyar dake tsakaninsu a yanzu ta kai dala biliyan 9.

Da farko kafin ya tafi Nijeriya, Rex Tillerson ya tattauna da shugaba Idris Deby na kasar Chadi game da barazanar kungiyar Boko Haram.

Kasashen da sakataren wajen Amurkan ya ziyarta sun hada da Habasha da Djibouti da Kenya da Chadi da kuma Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China