in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta baiwa Laberiya tallafin shinkafa
2018-03-13 09:33:20 cri

Kasar Sin ta baiwa Liberiya tallafin tan 1,243 na shinkafa a matsayin agajin gaggawa na abinci ga kasar.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar Laberiyan ta sanar da maraicen Lahadin da ta gabata, ta tabbatar da cewa, dukkan kwantainoni 50 da kasar Sin ta aike da su sun isa kasar, kuma tuni jami'an gwamnatin kasar ta Laberiya suka karba.

Mai rikon mukamin ministan harkokin wajen kasar Elias Shoniyin ya ce, sun samu wannan taimakon ne bisa ga bukatar da gwamntain kasar Laberiyan ta gabatarwa gwamnatin kasar Sin.

Shoniyin ya ce, wannan tallafin abincin zai taimaka wajen rage halin matsin rayuwa da ake fuskanta a kasar sakamakon karuwar farashin shinkafa a kasar, shinkafa ita ce abincin da mafi yawan 'yan kasar masu karamin karfi suka dogara kansa a Laberiyar.

Ya ce, sabuwar gwamnatin shugaban kasar George Weah, tana aiki ba kakkautawa wajen ganin ta daidaita farashin shinkafar, da nufin tabbatar da ganin al'umma masu karamin karfi a kasar suna iya sayen ta a farashi mai rahusa.

Fu Jijun, jakadan kasar Sin a Liberiya ya bayyana cewa, za'a raba shinkafar ne ga mutane mabukata, ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta taimaka wa kasar ta yammacin Afrika wajen noman shinkafar, da kuma bunkasa fannin aikin gona.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China