in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar adawa a Saliyo yana kan gaba
2018-03-12 13:46:35 cri

Hukumar zaben kasar Saliyo ta bayyana a jiya Lahadi cewa, 'dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar adawa ne ke kan gaba da kadan a bisa kwarya-kwaryar sakamakon zaben wanda aka kada a ranar 7 ga watan nan na Maris.

Julius Maada Bio, na babbar jam'iyyar adawa ta SPP ya samu kashi 43.33 bisa 100 daga cikin kashi 75 bisa 100 na sakamakon zaben wanda shugaban hukumar zaben kasar N'Ali Koroma, ya ayyana. Samura Kamara, na jam'iyyar APC mai mulkin kasar shi ne ke bi masa baya da kashi 42.57 bisa 100 na kuri'un da aka jefa.

Sai kuma Kandeh Yumkella, na jam'iyyar NGC wanda ya zo na uku da kashi 6.95 bisa 100.

Sama da mutanen kasar Saliyo miliyan 3 ne suka kada kuri'unsu a babban zaben kasar wanda aka kada a ranar 7 ga watan nan na Maris, inda ake zabar sabon shugaban kasa da majalisun dokoki da kuma majalisun kananan hukumomin kasar.

Idan ba'a samu wanda ya lashe kashi 55 bisa 100 na sakamakon zaben shugaban kasar a zagayen farko ba, za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben makonni biyu bayan sanar da cikakken sakamakon zaben shugaban kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China