Kakakin rundunar 'yan sanda Terna Tyopev, ya shaidawa manema labarai a Jos babban birnin jihar cewa, 'yan sanda sun kama wani makiyayi mai suna Muhammadu Musa Bimini tare da bindiga kirar AK-47 a ranar 8 ga watan nan.
A nasu bangaren, shugabanni a yankunan da al'amarin ya auku sun ce an kashe mutane da yawansu ya kai 25 yayin hare-haren.
Shugabannin sun kuma shaidawa manema labarai cewa har yanzu kwai wasu mutane da ba a gansu ba.
Hare-haren sun auku ne kasa da sa'o'i 24 bayan shugaban kasar Muhammdu Buhari ya kai ziyarar yini daya Jos. (Fa'iza Mustapha)