A cewar daraktan sashen ayyukan hukumar a Gaza wato Matthias Schmale, idan kasashe masu bada tallafi ba su bada sabuwar gudunmuwa don tallafawa hukumar gudanar da ayyukanta na kiwon lafiya da samar da ilimi ba, to ayyukanta za su fuskanci barazana ya zuwa watan Mayu.
Jami'in wanda ya soki kasashen duniya game da gazawa wajen warware matsalar 'yan gudun hijirar Falasdinu, ya ce kaso 77 cikin 'yan gudun hijirar Falasdinu miliyan 1 dake karbar tallafin abinci a Gaza, na rayuwa ne kasa da matakin talauci. (Fra'iza Mustapha)