in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun nuna yabo kan shirin ganawar shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa
2018-03-11 14:03:51 cri
Bisa labarin da aka samu, an ce, kafin watan Mayu na shekarar bana, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai gana da takwaransa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un, domin cimma burin kawar da makaman nukiliya a yankin Koriya na dindindin. Lamarin da yake samun yabo daga gamayyar kasa da kasa.

Dangane da wannan batu, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya fidda wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya nuna yabo matuka kan shirin ganawar shugaban kasar Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un. Kuma, kakakinsa Stephane Dujarric ya ce, babban magatakardan MDD ya nuna yabo matuka kan kwarewar shugabanci da shugabannin biyu suka nunawa al'ummomin kasa da kasa. Ya kuma jaddada cewa, MDD za ta nuna goyon baya ga bangarori daban daban da abin ya shafa kan dukkanin ayyukan da za su yi bisa kudurori na kwamitin sulhu na MDD, domin kawar da makaman nukiliya a duk fadin zirin Koriya cikin zaman lumana.

A ranar 9 ga wata kuma, ministan harkokin wajen kasar Burtaniya Boris Johnson ya yi maraba da ganawar da shugabannin kasar Amurka da kasar Koriya ta Arewa za su yi ta shafin intanet. Kana, fadar shugaban kasar Faransa ta fidda wani rahoto a ranar 9 ga wata cewa, shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump ta wayar tarho, inda ya nuna yabo matuka kan sanarwar da kasar Amurka ta fitar na yin shawarwari a tsakanin shugaban kasar da shugaban kasar Koriya ta Arewa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China