in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da kara haraji kan kayakin karafa da ake shigarwa kasar duk da adawar da kasashen duniya suka nuna
2018-03-09 12:45:38 cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya rattaba hannu kan shirin kara haraji kan kayakin karafa da langa-langa da ake shigar da su kasar, duk da adawar da 'yan kasuwa da abokan cinikayyar kasar suka nuna a fadin duniya.

Amurka za ta sanya harajin kaso 25 kan karafa da ake shigar da su kasar da kuma kaso 10 kan langa-langa. Shugaba Trump ya ce samun babbar masana'antar karafa da langa langa na da muhimmanci gaya ga tattalin arzikin kasar.

Harajin zai fara aiki ne cikin kwanaki 15 inda aka cire kasashen Canada da Mexico, har zuwa lokacin da za a sake cimma yarjejeinyar cinikayya cikin 'yanci ta kasashen arewacin Amurka wato NAFTA.

Shugaban ya ce za a dakatar da amfani da sabon harajin kan kasashen biyu, domin duba ko za su iya cimma yarjejeniyar ta NAFTA ko kuma a'a. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China