in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi kira ga kasashen Amurka da Koriya ta arewa da su yi shawarwari tun da wuri
2018-03-08 11:11:25 cri
A yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a bayyane take karara cewa, shawarar da kasar Sin ta gabatarwa kasashen Amurka da Koriya ta arewa, wato Amurka ta dakatar da yin babban atisayen soja, kana Koriya ta arewa ma ta dakatar da gwajin makaman nukiliyarta, hakan wata dabara ce mai amfani, wadda za ta samar da muhalli mai kyau wajen kyautata dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, musamman ma Amurka da Koriya ta arewa da su yi mu'ammala da shawarwari ba tare da bata lokaci ba. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China