An kiyasa kashe kudin kasar kimanin meticais miliyan 500 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 8.3 domin tsara dabarun yaki da rashawar tsakanin shekarar 2018 da ta 2022 da nufin inganta ayyukan hukumomin kasar da bin sahihiyar hanya wajen tafiyar da harkokin kudaden gwamnati da hukumomi masu zaman kansa a kasar. (Ahmad Fagam)