Kakakin ma'aikatar Geng Shuang ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na goyon bayan kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a ko da yaushe, kana, tana goyon bayan warware dukkanin sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da kuma gaggauta aikin kawar da makaman nukiliya daga yankin Koriya. A cewarsa, Sin na ganin hakan zai dace da moriyar bangarorin da abin ya shafa da kuma biyan bukatun al'ummomin kasashen biyu, sannan, zai tabbatar da kiyaye zaman lafiyar yankin baki daya.
Ya kuma kara da cewa, ana fatan kasashen biyu za su aiwatar da matakan da suka cimma ra'ayi guda a kai yadda ya kamata tare da gaggauta neman sulhu a tsakaninsu. Inda a nata bangaren kasar Sin, za ta bada gudummawa kan batun cikin himma da kwazo. (Maryam)