in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nijeriya ta musanta cewa kungiyar Boko Haram na rike da wani babban yanki a kasar
2018-03-07 09:14:56 cri
Babban hafsan sojin Nijeriya Lt. Janar Tukur Buratai, ya musanta ikirarin da ake cewa mayakan Boko Haram sun sake hadewa tare da karbe iko da wani babban yanki a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Fatakwal a jiya, Tukur Buratai, ya ce babu wani abu mai kama da sake bullowar kungiyar, yana mai cewa wasu daidaikun al'amura da suka faru ba su cancanci su tabbatar da sake bullowar kungiyar ba.

Ya ce dole ne kowane bangare na al'umma ya shiga cikin yaki da ta'addanci, yana mai bayyana matsalar a matsayin iftila'in da ya shafi daukacin kasar wanda dole ne a hada hannu wajen cimma nasarar kawar da shi.

Babban Hafsan ya kara da jadadda kudurin rundunar na ceto 'yan matan sakandaren Dapchi 110 da 'yan ta'addan suka sace a watan da ya gabata.

Tun a shekarar 2009, kungiyar Boko Haram ke kokarin kafa daular Islama a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, al'amarin da ya kai ga kisan mutane dubu 20 tare da tilasta wa miliyoyi tserewa daga matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China