Da yake jawabi a wani taro kan tsaro da ya gudana jiya a Abuja babban birnin kasar, Mansur Dan Ali, ya ce dole ne a yi dukkan mai yuwa dan kare sake aukuwar lamarin a nan gaba.
A ranar 19 ga watan Fabrerun da ya gabata, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne, suka sace 'yan mata dalibai 110 na kwalejin kimiyya da fasaha ta Dapchin jihar Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar.
Al'amarin na zuwa ne shekaru 4, bayan 'yan wannan kungiya sun yi wa sakandaren 'yan mata ta Chibok tsinke, inda suka sace fiye da 'yan mata 200
Har ila yau, Ministan ya ce akwai bukatar samar da ingantacciyar hanyar magance barazanar kutsen intanet. Saboda a cewarsa, galibin kungiyoyin 'yan ta'adda sun koma amfani da kafar intanet wajen jan hankali da daukar sabbin mambobi. (Fa'iza Mustapha)