in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Koriya ta Arewa ya gana da tawagar Koriya ta Kudu
2018-03-06 10:47:34 cri
Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya gana da membobin tawagar musamman ta kasar Koriya ta Kudu jiya Litinin, inda tawagar ta bayyanawa Kim Jong-un niyyar takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in, na gudanar da shawarwari tsakaninsu. Bangarorin biyu sun kuma yi musanyar ra'ayi, gami da cimma matsaya mai gamsarwa.

An ce, Kim Jong-un ya kuma bukaci da a shirya shawarwarin ba tare da bata lokaci ba. Shugaban tawagar Koriya ta Kudu, Chung Eui-yong, ya gabatar da wasikar da Moon Jae-in ya rubutawa Kim Jong-un.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China