Rahoton binciken wanda aka fitar a Dar es Salaam, birnin kasuwancin kasar Tanzania ya ayyana cewa, matakin ilmi a fadin nahiyar yana kara fuskantar koma-baya.
Rahoton ya ce, ko da yake an dan samu cigaba ta fuskar shigar da yara a makarantun firamare da karamar sakandare, to sai dai duk da haka, akwai yara kanana sama da miliyan 50 wadanda ba su zuwa makarantun, kuma mafi yawan wadanda suka yi dacen kammala karatunsu ba su samun kwarewar da za ta ba su damar samun kyakkyawar makoma a rayuwarsu ta nan gaba.
A cewar rahoton binciken, gwamnatocin kasashen Afrika suna kashe dalar Amurka 204 ne kacal a kan ko wane dalibin makarantun firamare, a bisa shekarar 2014, kasa da rabin kason da ake kashewa daliban firamaren a kudancin Asiya, yankin wanda shi ne na biyu mafi karancin kashe kudaden ga dalibai. (Ahmad)