in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron ganawa da manema labarai kan taron NPC karo na farko
2018-03-05 10:43:29 cri

Yau Litinin 5 ga wata, aka bude taro karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 13 a nan birnin Beijing, taron da zai jawo hankalin al'ummun kasashen duniya baki daya, kafin wannan, a yammacin jiya, an shirya taron ganawa da manema labarai karo na farko kan taron, inda sabon kakakin taron Zhang Yesui ya gabatar da jadawalin babban taron, kuma ya amsa tambayoyin da manema labarai na gida nan kasar Sin da kasashen waje suka yi masa kan wasu manyan batutuwan da suka fi jawo hankalin al'ummun kasashen duniya.

Zhang Yesui, mai shekaru 65 da haihuwa, sabon kakakin babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, shine mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya taba yin aiki a MDD bisa matsayinsa na manzon kasar Sin, kana ya taba kasancewa jakadan kasar Sin a kasar Amurka, yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya a jiya, da farko dai Zhang Yesui ya yi bayani kan jadawalin babban taron, shi ma ya bayyana cewa, babban taron NPC na bana yana da muhimmanci matuka saboda a karo na farko ne za a yi bikin rantsuwa a gaban tsarin mulkin kasa na kasar Sin, yana mai cewa, "Za a bude babban taron a safiyar ranar 5 ga wata, kuma za a rufeshi ne a safiyar ranar 20 ga wata, wato za a shafe kwanaki 15 da rabi ne ana gudanar da babban taron, gaba daya za a gudanar da taron ne bisa matakai goma, da farko dai za a duba rahoton aikin gwamnatin kasar, da rahoton shirin kasa, da kuma rahoton kasafin kudin kasar, daga baya za a duba daftarin gyaran tsarin mulkin kasar, da daftarin dokar sanya ido, haka kuma za a duba rahoton aikin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da rahoton aikin babbar kotun kasar, da rahoton aikin babbar hukumar gabatar da kara ta kasar, bayan haka, za a duba shirin yin gyaran fuska ga hukumomin majalisar gudanarwar kasar, a karshe dai za a gudanar da zabe tare kuma da nada jami'an hukumomin kasar ta Sin. A safiyar ranar 17 da 18 da kuma 19 ga wata, za a shirya cikakken taro karo na 5 da na 6 da kuma na 7 daya bayan daya, yayin wadannan cikakkun taruka 3, za a yi zabuka da kuma nada jami'an hukumimin kasar, bayan tarukan, za a shirya bikin rantsuwa a gaban tsarin mulkin kasa, wanda zai kasance karo na farko da za a gudanar da bikin a yayin babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tun bayan da aka fara aiwatar da tsarin rantsuwa a gaban tsarin mulkin kasar, ko shakka babu bikin zai kara kwarjinin tsarin mulkin kasar Sin yadda ya kamata."

An zartas da tsarin mulkin kasar Sin na yanzu ne a shekarar 1982, daga baya an yi masa gyaran fuska har sau hudu, Zhang Yesui ya ce, yayin wannan taro, za a sake yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, domin kara kyautata tsarinsa, ta yadda zai biya sabbin bukatun cigaban kasa a sabon zamanin da ake ciki, misali game da tanadin da aka yi kan wa'adin aikin shugaban kasa, ya ce, "Yanzu bisa ka'idar JKS da tsarin mulkin kasa, ba za'a kayyade wa'adin aikin babban sakataren JKS da shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na JKS da shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na jamhuriyar jama'ar kasar Sin ba, shi yasa tsarin mulkin kasar Sin ba zai kayyade wa'adin aikin shugaban kasar Sin ba, dalilin da yasa haka shine domin kiyaye kwarjinin kwamitin tsakiya na JKS dake karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, tare kuma da kara kyautata tsarin jagorancin kasar ta Sin."

Kan batun kara zurfafa gyaran fuska ga tsarin sanya ido, Zhang Yesui ya bayyana cewa, makasudin aikin shine domin kara karfafa jagorancin JKS kan aikin yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa, "Kwamitin sanya ido na kasar Sin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ne wadda ke da halayyar musamman ta kasar Sin, dokar sanya ido doka ce da aka tsara domin yaki da cin hanci da rashawa, a don haka aikin sanya ido yana da babbar ma'ana."

Ban da haka Zhang Yesui shi ma ya amsa tambayar da aka yi masa game da huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka a shekarar 2018 da ake ciki, yana mai cewa, "Na taba zama jakadan kasar Sin dake Amurka, na lura cewa, moriyar dake shafar sassan biyu tafi sabanin dake tsakaninsu, gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu itace hanya daya tak da ta fi dacewa, kasar Sin bata son yin takara da Amurka wajen ciniki, amma ba zata yarda a lahanta moriyarta ba."

Zhang Yesui ya jaddada cewa, bambanci da sabani ba za su jawo kiyayya ba, kasar Sin tana son sanya kokari tare da kasar Amurka domin ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba lami lafiya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China