Cikin wata sanarwa, Muhammadu Buhari ya ce harin ya nuna cewa 'yan ta'addan ba su da imani bare tausayi.
Shugaba Buhari ya jajantawa MDD da sauran hukumomin agaji dake aiki a Rann, inda ya ce harin na mastorata zai kara zaburar da kudurin gwamnati ne na kawo karshen kungiyar Boko Haram cikin kankanin lokaci.
A jiya Juma'a ne MDD ta tabbatar da kisan jami'an 3, inda ta ce akwai wani ma da ake fargabar ya mutu da kuma wani da aka sace yayin harin, har ila yau, wata jami'ar kiwon lafiya ta samu rauni.
A cewar kakakin MDD a Nijeriya Samantha Newport, dukkan jami'an da harin ya rutsa da su 'yan asalin kasar ne. (Fa'iza Mustapha)