Babbar mai shiga tsakanin rundunar sojin Nijeriya da kungiyar ta Boko Haram Aisha Alkali wakil ce ta bayyana haka a jiya Juma'a.
Aisha Alkali wadda Lauya ce kuma fitaciyar mai rajin kare hakkin dan Adam dake zaune a yankin na arewa maso gabashin kasar, ta ce tsagin Abu Musab Al-Barnawi ya tuntube ta a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya tabbatar mata cewa ya na rike da 'yan matan. A cewarta, 'yan matan suna nan cikin koshin lafiya.
Aisha Alkali da ake wa lakabi da 'mama Boko Haram' a Nijeriya, ta shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar cewa, shgugaban tsagin wato Al-Barnawi, ya yi alkawarin ba zai illata ko kashe 'yan matan ba.
A farkon wannan makon ne fitattaciyar lauyar mai rajin kare hakkin dan Adam ta gano wadanda suka sace 'yan matan, inda ta roki su sake su.
Ta ce tsagin kungiyar ya kira ta ne ta la'akari da rokon da ta yi musu.(Fa'iza Mustapha)