in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya la'anci harin da mayakan Boko Haram suka kaiwa wasu ma'aikatan agaji a Najeriya
2018-03-03 13:47:01 cri
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi tir da harin da mayakan kungiyar nan ta Boko Haram suka kai yankin arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya hallaka ma'aikatan bada agajin jin-kai uku.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar a jiya, Antonio Guterres ya jajantawa iyalan ma'aikatan agajin da suka rasa rayukansu, gami da gwamnati da jama'ar Najeriya.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa, hare-haren da aka kai wa fararen-hula gami da ababen more rayuwar jama'a, sun saba da dokokin jin kai na kasa da kasa, kuma ya zama tilas a yankewa wadanda suka kai harin hukunci mai tsanani.

Stephane Dujarric ya ce, yayin abkuwar harin, akwai ma'aikatan bada agajin jin-kai sama da arba'in a garin Rann na jihar Bornon Najeriya. kuma ya zuwa yanzu, dukkanin ma'aikatan sun janye daga wurin, sannan, an dakatar da ayyukan bada agajin.

Har wa yau, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadarai da harin ta'addanci da aka kai birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso jiya a Jumma'a.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China