in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta ce tattalin arzikinta zai karu da kashi 3.5 bisa dari a bana
2018-03-02 13:41:17 cri
Mashawarcin shugaban Nijeriya kan harkokin tattalin arziki Adeyemi Dipeolu, ya tabbatar da farfadowar tattalin arzikin kasar, bayan hukumar kididdigar kasar ta fitar da rahoto kan ma'aunin tattalin arziki na GDP na shekarar 2017.

Sabon rahoton da aka fitar, ya nuna kyakkyawan yanayin ingantuwar tattalin arzikin kasar, inda saurin karuwarsa ya kai kashi 1.92 bisa dari cikin watanni uku na karshen shekarar 2017, adadin ya karu idan aka kwatanta da na watannin uku da suka gabaci lokacin, wato tsakanin watan Yuli zuwa watan Satumba.

Haka kuma, adadin karuwar ayyukan gona ya kai kashi 4.23 bisa dari, yayin da aka samu kashi 3.92 bisa dari a fannin masana'antu, da kuma kashi 0.1 bisa dari a fannin sana'o'in ba da hidima. Baki daya dai, tattalin arzikin ya karu da kashi 2.76 bisa dari idan aka kwatanta da na tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2017.

Bugu da kari, abin da ya fi janyo hankali shi ne, karuwar hada-hada a fannin man fetur inda ya kai kashi 1.45 bisa dari a watanni ukun karshen shekarar 2017, bayan an samu raguwar wannan fanni tsakanin watan Yuni da Satumba. Lamarin dai ya kasance karuwa mafi sauri da aka samu tun daga shekarar 2015, wanda ya nuna cewa, yanayin tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da samun tagomashi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China