in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar matsala ta fuska uku yayin da ake kokarin kawo karshen rikicin Syria
2018-03-02 11:01:54 cri

A baya bayan nan, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, inda ya bukaci a tsagaita bude wuta a fadin kasar Syria a cikin kwanaki a kalla 30, kana ya yi kira da a dage kawanyar da aka yi wa yankin Ghouta na Gabas da sauran yankunan kasar. ban da haka kuma, duk da cewa rundunar sojojin Rashar ta sanar da cewa, za a tsagaita bude wuta na a kalla sa'o'i biyar a ko wace rana a yankin Ghouta na Gabas tun daga ranar 27 ga watan jiya, har yanzu bangarorin dake gwabzawa da juna a kasar ba su amince da wannan mataki ba.  

Yakin dake kasancewa a kasar Syria cikin shekaru kusan bakwai da suka gabata, ya kawo wahalhalu masu tsanani ga al'ummar kasar. Duk da cewa, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin tsagaita bude wuta a fadin kasar, cimma wannan buri na da wahala matuka. An lura cewa, akwai babbar matsala wajen kawo karshen yakin kasar. Daga yanayin da kasar ke ciki yanzu, ana iya ganin cewa, idan har ana son shimfida zaman lafiya a kasar to wajibi ne a warware matsalolin ta fannoni uku.

Da farko, dole ne a warware sabanin dake tsakanin rundunonin sojojin gida da na kasashen waje. A yanzu haka, sojojin gwamnatin kasar na kokarin kiyaye ikon mulkin kasar, yayin da rundunar sojojin adawa ke kokari tumbuke mulkin, kana dakarun kananan kabilun kasar suna gwabzawa da juna domin neman karin moriya, yayin da kuma rundunonin sojojin kasashen waje suke shiga tsakani. Sabili da haka, ana iya cewa, a cikin kasar ta Syira, ana yaki da ta'addanci, a sa'i daya kuma, ana fama da yake-yaken tsakanin bangarori daban daban, misali sojojin gwamnati da dakarun adawa, da dakarun kabilu da sojojin kasashen waje da sauransu. ko shakka babu, yanayin da kasar ke ciki yana da sarkakiya matuka. Haka kuma, abu ne mai wuya a iya daidaita matsalar cikin gajeren lokaci, saboda bangarorin dake gwabza fada a kasar, ba su da niyyar daina gaba da juna matukar ba su cimma burinsu ba. Ban da haka kuma, Rahotanni na cewa rundunonin sojin kasashen waje su ma ba za su daina nuna goyon baya gare su ba bisa dalilin moriyar kansu, lamarin da zai sa yanayin da ake ciki ya kara tsananta.

Na biyu, amincewa da juna a kasar abu ne mai wahala. tun bayan barkewar yaki a Syria, kasashen duniya suka gabatar da shirye-shirye iri daban daban domin kawo karshe yakin, tare kuma da shimfida zaman lafiya a kasar. Su ma bangarorin dake adawa da juna sun tattauna a tsakaninsu sau da dama karkashin shiga tsakanin MDD da sauran kasashen duniya, sai dai babu wani ci gaba da aka samu sabooda sun gaza aminta da juna.

Kawo yanzu, gwamnatin kasar Syria da dakarun adawa na kasar sun tattauna a tsakaninsu har sau tara, amma har yanzu ba su yarda sun tattauna kai tsaye fuska da fuska ba, sai manzon musamman na babban sakataren MDD Staffan de Mistura, dake tattaunawa da wakilansu bi da bi, daga baya ya mika ra'ayoyinsu ga juna.

Game da batun siyasar kasar, gwamnatin Syria da dakarun adawa sun gaza cimma matsaya, don ko a karshen watan Janairun bana, an gudanar da babban taron shawarwari tsakanin bangarori daban daban na fadin kasar a birnin Sochi na Rasha, ko da yake wakilan da suka halarci taron sun amince cewa, za a kafa kwamiti da zai tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar, tabbatar da kudurin abun ne mai wuya la'akari da wasu muhimman dakarun adawa dake nuna kiyayya ga babban taron.

Na uku, da wuya Rasha ta hada gwiwa da kasashen yamma yayin da suke kokarin daidaita matsalar Syira, saboda dukkansu suna son kara samun moriya a kasar, misali Rasha tana sa ran cewa, za ta kara yin tasiri a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar shiga tsakani a cikin harkokin Syria, yayin da Amurka har kullum ke kokarin yin takara da Rasha, shi ya sa yake da matukar wahala sassan biyu su yi hadin gwiwa ko da kuwa akan batun Syria ne.

Bugu da kari, yankin Gabas ta Tsakiya yana kusa da nahiyar Turai, saboda haka ba zai yiyu kasashen Turai kamar su Birtaniya da Faransa su daina tsoma baki a cikin harkokin Syria ba, su ma za su ci gaba da yin takara da Rasha kan wannan batu.

Duk da cewa, ana fuskantar wahalhalu da dama yayin da ake kokarin kawo karshen rikicin na Syria, ana fatan za a cimma burin wanzar da zaman lafiya a kasar ta hanyar siyasa wato ta hanyar tattaunawa karkashin jagorancin MDD.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China