in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin ECOWAS da AU da UN da EU, sun bukaci a kauracewa rikicin zabe a Sierra Leone
2018-03-02 09:43:49 cri
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS da Tarayyar Afrika AU da MDD da kuma Tarayyar Turai, sun bukaci a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a kasar Sierra Leone.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar jiya Talata, Hukumomin 4 sun ce su na bibiyar yadda shirye-shiryen zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisu da na kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Maris ke wakana.

Da suke maraba da kokarin da hukumar zaben kasar ta yi game da shirye-shiryen zabukan da tura jami'an sa ido na ciki da wajen kasar, hukumomin sun bayyana damuwa game da rikicin zabe da aka samu a baya-bayan nan a kasar dake yammacin Afrika.

Har ila yau, sun ce suna maraba da jajircewar masu ruwa da tsaki na kasar, na tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe kamar yadda ka'idojin kasar da kasashen waje suka tanada.

Sun kara da bukatar jam'iyyun siyasa da shugabanninsu su kauracewa kalaman tunzuri, kana su yi kira ga magoya bayansu su kauracewa ta da fitina.

Hukumomin da suka bukaci kungiyoyin al'umma da kafafen yada labarai su san irin muhimmancin da suke da shi, sun kuma yi kira ga bangaren shari'a da hukumomin tsaro, su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar nuna kwarewa da kauracewa bangaranci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China