Haka kuma, an ce, a daren ranar 26 ga wata, jiragen ruwan biyu sun tashi daga lardin Mai-Ndombe, sa'an nan sun nitse a kogin Congo sakamakon kadawar iska mai karfi da mamakon ruwan sama.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, mutane 108 sun tsira daga hadarin, yayin da mutane 14 suka bace. Haka kuma, wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ya nuna cewa, babu tabbas ko wadanda suka bace din za su tsira daga wannan hadari.
Akwai albarkatun tabkuna da koguna cikin kasar ta Congo(Kinshasa), kuma mazauna wurin su kan yi tafiye-tafiye cikin jiragen ruwa, amma, an sha fama da hadarurrukan nitsewar jiragen ruwa a kasar sakamakon lalacewar jiragen ruwa ko kuma daukar mutane fiye da kima. (Maryam)