in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Pakistan hudu sun rasu sakamakon harin kunar bakin wake
2018-03-01 11:00:23 cri
A daren jiya Laraba, an kai harin kunar bakin wake ga ma'aikatan rundunar sojojin tsaron kasar Pakistan dake binin Quetta na lardin Balochistan dake kudu maso yammacin kasar. Harin da ya haddasa rasuwar ma'aikatan rundunar 4, yayin da mutane 6 suka jikkata.

Wani jami'in rundunar ya bayyana cewa, dakarun sun kai hari a gaban sansanin rundunar dake yankin karkarar birnin Quetta, an kuma yi musayar wuta mai tsanani a wurin.

Bayan aukuwar harin, wasu rundunonin sojojin tsaro da masu ba da agaji sun isa wurin, inda suka toshe wurin da harin ya auku, sa'an nan suka fara neman wadanda suka taimakawa dakarun da suka kai harin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China