in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da gyaran fuska kan tsarin sa ido yadda ya kamata a kasar Sin
2018-02-28 10:53:49 cri

Za a bude taruka biyu wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taron majalisar bada shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin a nan birnin Beijing nan bada dadewa ba, yayin tarukan da za a gudanar a farkon wata mai zuwa, za a tattauna kan wasu batutuwa game da tsarin sa ido na kasar ta Sin.

Tun daga karshen shekarar 2016, aka fara gudanar da gyaran fuska kan wannan tsarin sa ido domin hana yaduwar cin hanci da rashawa a kasar Sin, bayan kokarin da ake, an samu babban sakamako a bayyane, a sa'i daya kuma, tsarin sa ido na kasar shi ma ya samu kyautatuwa a kai a kai.

A watan Nuwamban shekarar 2016, a hukumance ne, aka fara gudanar da gyaran fuska kan tsarin sa ido na kasar Sin a birnin Beijing da lardunan Shanxi da Zhejiang bisa mataki na farko, an kafa wasu hukumomin yaki da cin hanci da rashawa dake karkashin jagorancin jam'iyya mai mulki ta kasar wato JKS, domin gudanar da aikin sa ido ga daukacin jami'an dake aiki a hukumomin gwamnatin kasar, daga baya bi da bi ne birnin Beijing da lardunan Shanxi da Zhejiang suka kafa kwamitin sa ido, wanda zai yi aiki tare da hukumar ladaftarwa da sanya ido ta kwamitin tsakiyar JKS.

Daraktan kwamitin sanya ido na birnin Beijing Zhang Shuofu yana ganin cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake gudanar da gyaran fuska kan tsarin sanya ido shine a tsara shirin yin amfani da ikon sa ido, yana mai cewa, "Yanzu ana kokarin kara zurfafa gyaran fuska kan tsarin sa ido a kasar Sin, domin tabbatar da da'ar ma'aikata, musamman ma da'ar 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ana saran cewa, za a samu sakamako a bayyane a fannin yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar baki daya."

Tun daga watan Nuwamban bara, aka fara gudanar da gyaran fuska kan tsarin sa ido a fadin kasar, ya zuwa karshen watan Fabrairun bana, an riga an kammala aikin kafa kwamitocin sanya ido bisa matakai daban daban a fadin kasar yadda ya kamata, daraktan kwamitin sanya ido na birnin Beijing Zhang Shuofu ya bayyana cewa, wadannan kwamitocin da aka kafa bisa matakai daban daban zasu gudanar da ayyukansu bisa ka'ida, wato za su gudanar da ayyukan sanya ido da bincike da kuma yanke hukunci, ya ce, "Da farko dai kwamitocin sa ido zasu bada ilmi ga jami'an hukumomin gwamnati domin tabbatar da da'arsu, tare kuma da sa ido kan ayyukansu domin hana yaduwar cin hanci da rashawa, na biyu, zasu gudanar da bincike kan laifukan dake da nasaba da ayyukan jami'ai a hukumomin gwamnati, na uku, za su yanke hukunci ga jami'an wadanda suka sabawa doka, kana su mika wadanda suka aikata laifuka ga hukumomin shari'a domin su yi bincike kan su."

Bayan kokarin da aka yi a cikin shekara kusan guda data gabata, an samu sakamako mai faranta rai, bisa alkaluman da aka samu, an ce, a birnin Beijing da lardunan Shanxi da Zhejiang, adadin jami'an da aka sa musu ido ya karu da kaso 370 bisa dari da kaso 67 bisa dari da kuma kaso 83 bisa dari, haka kuma an samu babban cigaba wajen kama masu aikata laifukan cin hanci da rashawa da suka tsira zuwa kasashen waje.

Duk da cewa, an samu sakamako a fannin bisa mataki na farko, amma ana kokarin kyautata aikin domin samun sabon ci gaba, daraktan kwamitin sanya ido na lardin Zhejiang Liu Jianchao ya bayyana cewa, "Misali idan hukumomi biyu wato kwamitin sa ido da hukumar 'yan sanda suke gudanar da bincike kan wani mutumin da ake tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa, to ya zama wajibi su yi aiki cikin hadin gwiwa, ta haka zasu gudanar da aikin lami lafiya."

Yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da zai gudana a wata mai zuwa, za a duba da kuma tattaunawa kan daftarin gyaran tsarin mulkin kasar Sin da daftarin dokar sa ido na kasar, ko shakka babu lamarin zai sa kaimi kan aikin sa ido a kasar ta Sin, daraktan kwamitin sanya ido na birnin Beijing Zhang Shuofu ya bayyana cewa, za a kara zurfafa gyaran fuska kan tsarin sa ido a kasar domin samun cikakkiyar nasara a fannin yaki da cin hanci da rashawa, ya ce, "Za a kara karfafa aikin sa ido a nan kasar Sin, kuma za a kara kyautata aikin hukumomin ladaftarwa, da sanya ido, da aikin hukumomin shari'a na kasar, tare kuma da kara kyautata tsarin sa ido a fadin kasar, ta yadda za a samu cikakkiyar nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar ta Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China